Mun tantance mutane 800 cikin 1200 da suka nemi shiga shirin tura ɗalibai kasashen waje – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin fara daukar nauyin daliban manyan makarantu 1,010 a gida da waje a kashi na farko na tallafin karatun da zata bayar.

 

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr. Yusif Ibrahim Kofar Mata, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin kwamishinan yada labarai.

Talla

Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamishinan ya bayyana cewa an kafa kwamitin tantancewa na sake dawo da shirin daukar nauyin daliban da suka kammala karatu a Kano domin samun digiri na biyu a jami’o’in cikin gida da na ketare, an kafa tare da kaddamar da kwamitin a ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Tsaftar Muhalli: Zamu haɗa kai da shugabannin kasuwani a kano – Amadu Danzago

Ya kara da cewa, kwamitin ya karbi takardun neman shiga cikin shirin daga mutane sama da 1200, Kuma ya zuwa yanzu an tantance sama da mutane 800, kuma har yanzu ana cigaba da tantancewar kuma za a fitar da cikakkun bayanai na wadanda suka sami nasara nan ba da jimawa ba.

“Yana da matukar muhimmanci a sanar da al’ummar Kano cewa, dawo da wannan shiri da gwamnatin Abba Kabir Yusif ta yi, ba wai kawai don samawa ‘yan jihar Kanon takardar shaidar kammala digiri ba, a’a, a’a, a’a, shirin zai karawa matasanmu kwarin gwiwa da kuma kara samun damammaki a fannoni daban-daban waɗanda wataƙila za su iya taimakawa wajen sauya matsayin jiharmu a idanu duniya”.

Kwamishinan wanda kuma shi ne sakataren kwamitin maido da manufofin Kano na bayar da tallafin karatu ya bayyana cewa maido da manufar bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar Kano don yin manyan digiri a ciki da wajen kasar nan an yi shi ne da niyyar bunkasa rayuwar al’ummar Kano da Nigeria baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...