Cire Tallafin Mai: Za a yi ƙarin kuɗin burodi a Najeriya

Date:

Ƙungiyar masu gidajen burodi a Najeriya ta ce za ta ƙara farashin burodi da kashi 15 cikin ɗari daga ranar 24 ga watan Juli.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan kammala taron shugabanninta na ƙasa, ƙungiyar ta ‘Association of Master Bakers and Caterers of Nigeria’ ta ce ta ɗauki matakin ne bayan la’akari da nunnukawar farashin kayan aiki.

Talla

Sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Mansur Umar ta ce tashin farashin ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tarayya ta yi.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya nemi Majalisar Wakilai ta sahale ya kashe Naira Biliyan 500 don Tallafawa Yan Nigeria

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a cikin jawabinsa na karɓar mulki.

Lamarin ya haifar da tashin litar man fetur daga kimanin naira 200 zuwa sama da naira 500 a faɗin ƙasar, wani abu da ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan masarufi.

BBC Hausa ta rawaito Ƙungiyar ta ce abubuwan da take amfani da su wajen gudanar da sana’ar, waɗanda suka haɗa da man fetur, da gas, da fulawa, da suga da sauran su duk sun yi tashin gwauron zabi.

Haka nan ƙungiyar ta koka kan yadda hukumomi daban-daban a ƙasar ke karɓar haraji, kala-kala, wani abu da ke ƙara saka masu gidajen burodin cikin matsi.

Kan haka ne ta ce “An umurci dukkanin shugabannin ƙungiyar na yanki su tabbatar cewa ƴaƴan ƙungiyar sun bi wannan umarni, har sai idan sun samu wani sabon umarnin daga uwar ƙungiyar ta ƙasa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...