Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Majalisar wakilan Nigeria ta bukaci hukumar kula da jami’o’i ta kasar (NUC) da ta dakatar da aiwatar da karin kudaden karatun jami’o’i.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala daga Jihar kano Aliyu Sani Madaki (NNPP-Kano) ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar a ranar Talata.

Majiyar Kadaura24 Solacebase ta ruwaito cewa Madaki wanda ya bayyana cewa jami’o’in da suka kara kudadensu sun hada da Jami’ar Bayero ta Kano; Jami’ar Najeriya, Nsukka; Jami’ar Uyo; Jami’ar Maiduguri; Michael Okpara University of Agriculture, Umudike; da Jami’ar Tarayya da ke Dutse da dai sauransu.
‘Yan majalisar yayin zaman nasu sun nuna damuwarsu kan yadda akai karin kudaden jami’o’in a dai-dai lokacin da al’umma suke cikin halin kakanikayi sakamakon talauci, hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, da tashin farashin man fetur a baya-bayan nan.
‘Yan majalisar sun kuma yi nuni da cewa karin kudin jami’o’in na iya kara ta’azzara halin da kasar nan ke ciki, ganin cewa tuni dalibai suka fara yin barazanar da ka iya haifar da tada kayar baya ga Gwamnatin Tarayya, tare da haifar da mummunan sakamako ga kasar baki daya.
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta janye karin kudin makaranta da aka yi a makarantun sakandare na kadaka wato Unity Secondary School.