Zamfara: Gwamna Lawal ya rage yawan ma’aikatun jihar

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umurnin rage yawan ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16.

 

Lawal ya ce an dauki matakin ne don sauya fasalin ma’aikatun gwamnati don samar da ayyuka masu inganci a jihar.

Talla

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a sashihin shafin sa Facebook a ranar Alhamis, ya kara da cewa sake fasalin gwamnatin jihar ya yi daidai da manufarsa ta samar da majalisar zartarwar mai inganci da za ta rage kashe kudaden gwamnati don wadata al’ummar Zamfara da aiyukan cigaba.

Bidiyon Dala: Ganduje ya Magantu kan Gayyatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi masa

Ya rubuta: “A wani bangare na yunkurin gwamnatina na sauya fasalin ma’aikatun gwamnati don samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar mu ta hanyar rage kashe kudaden gwamnati, na ba da umarnin sake fasalin da rage yawan ma’aikatunmu daga 28 zuwa 16.

“An yi hakan ne bisa kudirina na samun majalisar zartarwar mai inganci wacce za ta rage tsadar harkokin mulki tare da samar wa jama’armu aiyukan raya kasa da ci gaban al’umma”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...