Kotu ta hana gwamnatin Kano, ƴansanda da DSS daga kama Ganduje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar Kano da jami’anta da ƴan sanda da ƴan sandan farin kaya da dai sauran hukumomin tsaro daga kama tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da duk wasu makimusantan sa.

 

Alkalin kotun, Mai shari’a A. M. Liman, a cikin takardar umarnin, mai dauke da kwanan wata 6 ga Yuli 2023 ya amsa wa masu shigar da korafin bukatar su.

Talla

“Wadanda ake kara ko su da kansu, ko kuma ta hanyar jami’ansu,jami’ansu, jami’an tsaron su, masu zaman kansu ko wani mutum ko gungun mutane kar su musgunawa, tsoratarwa, gayyata, barazanar kamawa, kamawa ko tsare wanda ya shigar da korafi, ko ‘ya’ya ko wani daga cikin danginsa, ko duk wanda aka nada wanda ya yi aiki a karkashin kulawar mai korafi ko kuma ya karbe kadarorin mai korafi da karfi ko ‘ya’yansa ko wani daga cikin danginsa, ko duk wanda aka nada wanda ya yi aiki a karkashin gwamnatin mai korafi har sai an yanke hukunci a kan neman hanawar”. A cewar umarnin kotun

Hotunan yadda Sanata Barau Jibril ya jagoranci zaman majalisar dattawa

 

“Cewa umarnin wucin gadi zai yi aiki har zuwa lokacin da za a saurari ƙorafin da aka shigar a kan tauye ƴancin ɗan adam zuwa ranar 14 ga Yuli, 2023.

Wadanda aka baiwa umarnin za a ba su kundin umarnin sa’o’i 36 daga yau,” in ji alkalin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...