Muna bukatar gwamnan Kano ya kwato mana tashar Malam Kato a aka sayar a baya – Kungiyar direbobi

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen jihar kano dake tashar mota ta Malam Kato, ta koka da yadda gwamnatin da ta gabata ta siyar da tashar tare da gineta ba bisa Ζ™a’ida ba.

Jami’in yada labaran kungiyar Alhaji Samaila Giredi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, dangane da halin da ‘ya’yan kungiyar suka tsinci kansu a ciki.

Talla

Alh. Samaila Giredi, ya bayyana cewa, sakamakon gine wajen da aka yi,ya sanya wasu motocin sun fito wajen tashar domin neman gurin tsayawa,inda matasa da dama da magidanta suka rasa hanyoyin cin Abincinsu,Wanda haka babbar barazana ce ga rayuwar al’ummar jihar kano musamman matasa.

Bidiyon Dala: Ganduje ya Magantu kan Gayyatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi masa

Yace ashar malam Kato,Tsohon Gwamnan jihar kano, DR. Rabiu musa kwankwaso ne ya samar da ita sakamakon taso direbobi daga shataletalen Bata domin su bar kan hanya, amma abun mamaki sai ga shi gwamnatin da ta gabata ta cefanar da tashar malam Kato.

 

Hotunan yadda Sanata Barau Jibril ya jagoranci zaman majalisar dattawa

“Tashar malam Kato, tashace da baki suke zuwa domin hawa mota Dan yin tafiye-tafiye kamar kasuwar singa da sabon gari da kofar wambai da kuma suran kasuwanni dake fadin jihar kano, Amma yanzu maganar da nake maka gwamnatin jihar kano da ta gabata ta siyarwa wasu mutane masu hannu da shuni, kuma haka na nuni da cewa babu tausayi ga masu karamin karfi da suke cin abinci a wannan tasha” . Inji Giredi

Shugaban ya roki gwamnatin jihar kano da a yanzu haka take kwatowa wadanda aka zalunta hakkokinsu, da ta waiwayesu domin tunawa da Tashar malam Kato kasancewar kungiyar ta baiwa Gwamnatin cikakken goyan baya har Allah yasa aka kafa.

Haka zalika kungiyar tace, ba za ta gajiya ba wajen yin kiraye-kirayen gwamnati mai ci karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta taimaka don dawo musu da tasharsu.

Kungiyar ta jaddada cewa,a shirye take wajen ci gaba da baiwa gwamnatin cikakken goyan baya da hadin kan daya kamata, musamman domin dawowa da Talakawan jihar kano hakkokin su .

“Dubbannin al’umma ne suke cin abinci a wannan tasha, kuma tashar ta magance cunkoson ababen hawa, amma fito da su da aka yi ya haifar da matsaloli cinkoson ababan hawa, wanda wannan na daga hangen nesa da Dr.. Rabiu Musa Kwankwaso na Samar da tashar don samar da aiyukan yi ga matasa da kuma rage cunkoso a tituna”. Sama’ila Giredi

Daga karshe kungiyar ta yabawa Gwamnatin jihar kano, bisa Namijin kokarin da take yi na ganin ta karbowa al’ummar jihar kano hakkokinsu da aka kwace, ba tare da an samar musu da mafita ba domin dogaro da kawunansu da rage masu zaman kashe wando a tsakanin al’umma, wanda rashin Sana’a ke haifar da gagarumar matsala da aikata abubuwa marasa kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related