Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha albashin sallamar duk kwamishinoni da ya gaza yin abun da ya dace a cikin watanni shida .
” Ku sani na dauko ku ne na baku wanann mukamin bisa kwarewar ku da chanchantarku , don haka duk wanda ya bamu Kunya a cikin watanni shida zamu sauke shi mu nada wani”. Inji Abba Gida-gida

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci taron majalisar zartarwar ta jihar kano, wanda aka gudanar a karamin dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano.
Gwamna Yusuf ya ja hakalin kwamishinonisa da cewar kada su Yi Mundahana da dukiyoyin Alummar jihar Kano.
Zargin Almundahana: Hukumar yaƙi da cin haci ta kama kwamishinan Ganduje da wasu mutane 5
” Ku guji sanya kanku a cikin duk wani abu na Almundahana da dukiyoyin al’umma, domin ba zamu bar duk wanda muka samu da cin Amana al’ummar jihar kano da suka zabe mu ba.
Kadaura24 ta rawaito cewar Gwamna Yusuf ya ce duk kwamishinan da gwamnati ta same shi da Mundahana da dukiyoyin al’umma nan da watanni shida masu zuwa tabbas zai bar mukaminsa