Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Wata matar aure, mai suna Latifat Musa, ta roki wata kotu a Ilorin dake jihar kwara, data raba auren su da mijinta saboda yawan cuta da take yi da kuma yawan bari da ta ke yi.

Mai shigar da kara, ta shaida wa kotun cewa tana jinyar cututtuka daban-daban tun bayan da ta auri mijinta mai suna Kareem, shekaru uku da suka wuce.
“Ina rokon wannan kotu mai albarka da ta raba aurena da mijina, saboda yawan rashin lafiya kala daban-daban da na ke yi ga kuma yawan barin cikina kuma tun da mukai aure ban haihu ba ,” inji ta.
Yadda Jam’iyyar APC ta Gabatar da Shaidu 5 Cikin 300 ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan Kano
Alkalin kotun, Aminullahi AbdulLateef, ya bayar da umarnin a yi wa wanda ake kara bayani dalla-dalla a kan karar da matar tasa ta kaisa.
Mai shari’a AbdulLateef ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 14 ga watan Agusta.