Makon ma’aikatan jinya: Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta ziyarci wani asibiti a kano da bada tallafi ga masa lafiya

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

 

Shugaban kungiyar masu jinya da aikin ungozoma na ƙasa reshen jihar kano Ibrahim mai karfi Muhammad ya yabawa ma’aikatar lafiya ta jihar saboda yadda ta samar da managartan kayan aiki a asibitin Gandun albasa daka karamar hukumar birnin Kano.

 

” Babu na ji farin ciki a raina Saboda irin managartan kayan aikin da na gani a wannan asibitin, wadanda a baya sai dai ka gansu a manyan asibitin jiha, amma yanzu gasu a kananan asibiti irin wanna”. Inji Ibrahim mai karfi

Talla

Ibrahim mai karfi ya bayyana hakan lokacin da suka ziyarci asibitin, a wani ɓangare na bikin tunawa da irin gudunmawar da masu aikin jinya da ungozoma suke baiwa al’umma na bana.

Zargin Almundahana: Hukumar yaƙi da cin haci ta kama kwamishinan Ganduje da wasu mutane 5

Shugaban ya kara da cewa kayan gwajin manyan cututtuka da ya gani a asibitin ya kwarin gwiwar ana samun cigaba a fannin kula da lafiyar al’ummar jihar kano, kuma hakan zai magance yawan mace-mace da ake samu sakamakon karancin kayan gwaje-gwaje a jihar.

Yadda Sanata Rufi’i Hanga da Aliyu Madakin gini suka sami mukamai a Majalisar kasa

“Ya zama wajibi mu yabawa ma’aikatan wannan asibiti na Gandun albasa, saboda yadda muka ga suna jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora musu don inganta lafiyar al’ummar yankin da suke aiki”. A cewar Ibrahim mai karfi

Yace bayan ga wannan ziyarar zasu kuma zuwa wani asibitin duk a karamar hukumar Birni domin ganin halin da asibitin yake ciki da Kuma ba da tallafi ga marasa lafiya.

A yayin ziyarar ta su kungiyar ta rabawa marasa lafiyar dake kwance a asibitin kaya kamar su : kunguzun yara da kananan wanduna na yara da dai sauransu, sannan suka bukaci wadanda aka baiwa kayan da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...