Saudiyya ta tsare sama da mutane 17,000 da suka yi yunƙurin hajji ba tare da izini ba

Date:

 

Hukumomin Saudiya sun kama tare da tsare mutum 17,615 da suka yi yunƙiurin yin aikin hajjin ba tare da izini ba.

 

Jaridar Saudi Gazzet ta ambato Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin bana Lt. Gen. Muhammad Al Bassami na bayyana haka, yama mai cewa 9,509 daga cikinsu mutane ne da suka saɓa ka’idar bizar aiki da ta zaman ƙasar.

Tallah

Ya ce an kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.

BBC Hausa ta Al-Bassami ya ce hukumomin ƙasar kuma sun tisa ƙeyar mutum 202,999 da suka yi yunƙurin shiga ƙasar don gudanar da aikin hajjin ba tare da izini ba.

Hotuna:: Yadda Sarkin Kano ya fita hawan Dorayi

Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin ya kuma yaba wa askarwan ƙasar bisa jajircewa da ya ce sun yi a lokacin gudanar da wanna gagarumin aiki cikin ƙwarewar aiki da basira.

Dokokin Saudiyya sun tanadi cewa duk mutumin da ke zaune a ƙasar, dole ne ya nemi izinin hukumomi idan yana son gudanar da aikin hajji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...