Da dumi-dumi: Muhuyi ya kwato motocin kwashe shara 13 da suka bata a gwamnatin data gabata

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado ta kwato wasu motocin kwashe shara guda goma 12, mallakin gwamnatin jiha.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta bayan mayar da Muhuyi Magaji kan mukaminsa yasha alwashin zai yi aiki ba sani ba sabo wajen ganin an kwatowa Mai hakki hakinsa.

Tallah

Motocin wadanda yanzu haka suna cikin hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano , kuma mallakin na ga hukumar kwashe shara ta jihar kano.

Hotuna:: Yadda Sarkin Kano ya fita hawan Dorayi

Yayin da ya ziyarci hukumar domin ganewa idanunsa motocin da aka kwato, kwamishinan harkokin Sufuri da gida na jihar kano, Engr. Muhammad Diggwal yace motocin an rasa su ne tun a gwamnatin data gabata, wanda hakan tasa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin nemo su duk Inda suke.

” Yanzu haka wadannan motocin ga su wanann hukumar ta kwato su daya bayan daya, Kuma naga wasun su ma an fara sauya musu fasali kuma cikin su har da katafila guda daya, Babu shakka wannan Abu da akai an yi abun daya dace koma zamu tabbatar al’ummar jihar kano sun cigaba da morarsu”. Inji Diggwal

Engr. Muhammad Diggwal yace zasu jira hukumar ta kammala bincike akan yadda aka motocin suka bace, ya yake da alhakin batan nasu, sanann sai hukumar ta ɗauki matakin da ya dace akan Wanda aka samu da laifi, Kuma a basu motocin don su cigaba da amfanar al’ummar jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...