Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Sauraron Korafe-korafen Al’umma da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), domin kammala wa’adinsa.
Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yada labaran gwamnan jihar ta Kano.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada mukaddashin mai magana da yawunsa
Sanarwar ta bayyana cewa Barista Muhuyi zai koma kan aikinsa ne nan take.
Idan za a iya tunanwa, gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Gnaduje ta dakatar da Muhuyi tare da tsige shi daga mukaminsa bayan majalisar dokokin jihar ta ce tana da shakku kan yadda yake gudanar da ayyukansa