Hajjin bana: An buƙaci wasu maniyyatan Nigeria su koma gida

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wasu maniyyata aikin hajji a Najeriya, sun koka dangane da yadda aka umarci wasunsu, su koma gida, saboda ba za su samu damar zuwa aikin hajjin bana ba, duk kuwa da biyan kuɗin aikin hajjin ta hanyar adashin gata.

Maniyyatan sun ce hakan ya faru ne bayan sun kwashe makonni a sansanin alhazai na Abuja.

Daya daga cikin maniyattan da lamarin ya shafa ta bayyana wa BBC Hausa cewa ta shafe fiye da kwanaki goma a sasanin alhazan babban birnin tarayya Abuja, amma har yanzu ba ta san makomarsu ba, sakamakon rashin wani bayani daga bangren mahukunta.

Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai

“Ga shi muna zaune ba su yi magana ba, na fara magana sai aka yanke waya, an ce min na yi hakuri na wuce gida,”

“Shi ne na ce me ya faru da za ka ce na wuce gida bayan na zauna sati uku, kuma sai a ce min na wuce gida, mene ne ya faru? Daga nan sai ya yanke waya.”

Kungiyar tsofaffin Daliban MAAUN ta wayar da kan dalibai mata hanyoyin da zasu kare kansu daga cututtuka

“Idan gwamnati za ta taimake mu, muna so, tunda ga shi dai dukkanmu ba mu wuce ba, muna da yawa da maza da mata.

Tallah

A wani taƙaitacan labari da darekta a hukumar alhazan Najeriya, Abdullahi Magaji Harɗawa ya yi wa BBC Hausa, ya ce maniyyatan da ke wannan koke sun fito ne ba tare da an kira su ba.

Sai dai ya ce hukumar alhazan na ɗaukan mataki.

“Alhazai ne waɗanda suka yi rajista ƙarƙashin ‘tour operators’, akwai jirginsu da aka ɗaukar musu na musamman wanda zai yi jigilar su.”

“kamfanin da aka fara da su, sun zo sun fara kuma sun gaza, amma yanzu ana shirya wani jirgin da zai zo ya kwashe su.”

“Kowane jirgi akwai lokacin da yake tashi, saboda da haka idan wasu sun zo ba tare da an kira su ba, wannan su suka kawo kan su.”

Ya kuma yi alƙawarin cewa za su tabbatar cewa an kwashe dukkanin alhazan zuwa Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...