Dan majalisar Ungoggo da Minjibir biyawa ɗalibai 100 kuɗin jarabawar NECO

Date:

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe

 

A Karon farko zazzaban dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo, Alhaji Sani Adamu Wakili ya biya wa daliban kananan hukumomin Minjibir da Ungoggo su 100 kudin jarrabawar NECO.

 

Alhaji Sani Adamu Wakili, ya bayyana cewa, tun a lokacin yana yakin neman zaben sa yayi alkawarin bada fifiko ga fanin ilimi, harkokin kiwon lafiya bada ruwan sha da kuma gyaran titunan kananan hukumomin.

Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai

Ya Kara da cewa, akwai bukatar masu ruwa da tsaki na kananan hukumomin Minjibir da ungogo su tabbata sun bada hadin kan daya kamata, domin ganin an cimma nasarorin da aka sanya a gaba.

Bayan komarwasa makarantar Islamiyya dattijo dan shekaru 60 ya sauke Alqur’ani a Kano

Sani Wakili yace zai yi aiki kafada da kafada da gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma yan majalisun na kananan hukumomin Minjibir da Ungogo dan ganin kananan hukumomin sun ciri tuta a fanin ilimi.

Kimanin dalibai hamsin hamsin ne daga kananan hukumomin Ungoggo da Minjibir suka amfana da kyautayin dan majalisar tarayyar.

Tallah

Tunda fari da yake nasa jawabin, shugaban kwaminitin bada tallafin karatun Dakta Surajo Suleman ya bayyana cewa, an biyawa daliban kudin jarrabawa ne a sakamakon faduwar da suka yi a jarabawar kwalifan ta wannan shekarar .

Ya Kara da cewa, kwaminitin nasu ya kewaya dukkanin makarantun dake kananan hukumomin Minjibir da Ungogo domin zakulo daliban maza da mata don biya musu kuɗin

A nasu jawaban shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomun Minjibir da Ungogo, Abubakar Ibrahim Abubakar dakuma Alhaji Bilyaminu Musa Adamu Bachirawa, sun bada tabbacin cewa zasu aiki da zababban dan majalisar tarayyar a ko wane lokaci.

Wasu daga cikin daliban da suka fito daga kananan hukumomun Minjibir da ungogo da suka amfana da tallafin biyan kudin jarrabawar ta NECO, sun bayyana farin cikin su tare da godewa zababban dan majalisar tarayyar, Alhaji Sani Adamu Wakili.

Taron dai ya gudanar a cibiyar yada addinin musulinci ta Karamar hukumar ungogo, wanda Kuma ya samu halartar al’umma da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...