Ƙungiyar ƙwadago za ta sake ganawa da gwamnatin Najeriya kan cire tallafi

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu a Najeriya za su sake ganawa da jami’an gwamnati don kokarin ganin sun amince da sabon mafi karancin albashi da kuma wasu bukatu na ma’aikata bayan da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur.

 

Janye tallafin ya jawo tashin farashin mai da tsadar sufuri.

Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai

Ƙungiyar ƙwadago da TUC a Najeriya ta ce yau ne wa’adin da ta ba gwamnatin tarayya ke cika, kan bukatarta mayar da mafi karanci albashi naira dubu 200 sakamakon janye tallafin mai.

Ƙungiyar ta ce bukatar biyan mafi kakantar albashin naira dubu 200 na cikin bukatun da ta mika wa gwamnatin Tarayya, domin ragewa ma’aikata raɗaɗin wahalar janye tallafin mai da sabuwar gwamnatin ta yi.

Comrade Nuhu Toro, sakatare janarar da kungiyar ya faɗawa BBC cewa suna kan bakansu akan albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 200 wa ƙaramin ma’aikaci a Najeriya domin tsadar rayuwar da mutane suka shiga.

Ya ce “Farashin kayayyaki da rayuwa ma gaba daya tsada ya keyi, saboda haka gwamnati ba ta da hujja illa ta ƙara ma ma’aikata mafi ƙanƙantar albashi na naira dubu 200 domin su ma’aikata su suke ƙirƙirowa ta arzikin ƙasa”.

“Gwamnati za ta iya biyan wannan albashin idan ta rage almubazaranci, idan ta rage sama da faɗi da dukiyan talakawa, kuma idan ta rage kashe kuɗi a kan abubuwan da bai kamata ba.”

Toro ya dai ƙara da cewa dole ne gwamnati ta rage yawan kashe kudin da take yi, shi ne za ta sami yanda za tayi ta biya ma’aikata albashi mafi ƙanƙanta naira dubu 200.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...