Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano ta bada tukuicin kujerar makka da takardar daukar aiki na dindin ga wani mutum da ya tsinci kuɗi har Naira miliyan goma sha shida a harabat hukumar .
Tun da fari dai mutumin mai suna Ɗangezawa ya bayyana wa majiyar kadaura24 Radio Kano cewa da misalin ƙarfe goma na daren ranar Alhamis ya tashi zai tafi gida sai ya ci karo da wata leda baƙa a daure, da ya duba sai ya ga Dalar Amurka mai tarin yawa nan da nan hankalin sa ya tashi ya dauki ledar ya fasa tafiya gida, ya kwana a ofishin hukumar.
Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu
“Da gari ya waye sai na kaiwa shugaban hukumar Alhaji lamin Baba danbaffa shi ma hankalin sa ya tashi nan da nan aka bincika aka kuma tarar da ashe kudin guzurin maniyyatan ƙaramar hukumar birnin ne, nan take aka karbi wadancan kudade aka mika su ga jami’in kula da alhazzai na ƙaramar hukumar birnin”. Acewa Dangezawa
Kadaura24 dai ta gano Ɗangezawa ya shafe shekaru ashirin da daya yana aikin wuccin gadi ( casual) a hukumar, yanzu haka dai an bashi takardar aiki ta din-din (Permanent and Pensionable) an kuma yi masa alkawarin Kujerar aikin Hajji baɗi idan Allah ya kaimu.