Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wasu masana sun tono kayyakin tarihi a Jamus sun gano wani hubbare na magabata.
Sun gano wani takobi a gefen wani kabari a kudancin birnin Nördlingen. Jami’ai daga hukumar da ke bibiyar kayayyakin tarihi sun ce takobin nanan lafiya ƙalau har yanzu yana kyalli.

Masanan sun kuma gano kwarangwal ɗin mutum da na wata mace da na yaro a gefen hubbaren tare da wannan takobi.
Har yazu masanan ba su kai ga gano alaƙar da ke tsakanin mutanen ba.
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Masana kayyakin tarihi a Jamus sun haɗa irin wannan takoɓi abu ne mai wuya, saboda an haɗa ta da tsagwaron ƙarfe ba ha’inci gabanta da bayanta.
Sun kuma ce a lokacin da aka haɗa ta an yi ta ne ba don ado ba.