Ɗalibai sun yi zanga-zanga kan garkuwa da ‘yan uwansu a Zamfara

Date:

 

Daliban Jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zanga don nuna ɓacin ransu kan sace ‘yan uwansu ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka yi a jihar.

 

Masu zanga-zangar sun fara taruwa ne tun daga Damba zuwa Sabon-Gida da ke makwabtaka ta jami’ar.

Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso

Matafiya da dama ne suka maƙale a lokacin da fusatattun ɗaliban suka toshe babbar hanyar Gusau zuwa Funtua.

Duk da tarin jami’an tsaron da ke birnin Gusau, ɗaliban sun toshe babbar hanyar da ke haɗa jihar da jihohin Sokoto da Katsina da kuma jihar Kaduna.

Tallah

Daliban sun ce a ranar juma’a da daddare masu garkuwa da mutanen sun sace ‘yan uwansu ɗalibai a garin Damba da ke wajen birnin Gusau.

A ranar Litinin ne ake sa ran fara jarrabawa a jami’ar, to sai dai ɗaliban sun ce ba za su bari a fara jarrabawar ba, har sai an kuɓutar da ‘yan uwan nasu.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...