Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya taya tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari murnar kammala wa’adin mulkinsa lafiya.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci tsohon shugaban kasar a gidansa dake Daura domin yi masa fatan alheri sakamakon kammala mulkin sa lafiya .
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Mai Martaba Sarkin na Kano yace a mulki irin na babbar kasa tarayyar Najeriya kuma Buharin yayi shekara takwas yana gudanar da mulki abun a taya shi murna ne kamar yadda ya fara lafiya kuma ya kammala lafiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24.
Yace a tsawon shekara Takwas dole ayi dai dai ko akasin haka, adon hakane yayi fatan samun rahama da yafiyar ubangiji Allah.