Sama da Mutane 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Yanzu haka ana ci gaba da aikin nemo gawarwakin sauran mutane da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Kwara a Najeriya.

 

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya kife ne a ranar Lahadi da daddare, inda yake ɗauke da mutane kimanin 300 waɗanda suka fito daga wajen biki.

Da dumi-dumi: Falgore ya zama Shugaban majalisar dokokin jihar Kano

Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin jihar Kwara, wadda mai magana da yawun gwamnan jihar ta sanyawa hannu ta ce jirgin na ɗauke ne da mutane waɗanda suka fito daga garin Egboti na jihar Neja kan hanyarsu ta zuwa Ƙaramar Hukumar Patigi a jihar Kwara.

Sanarwar ta ce mutanen da lamarin ya rutsa da su ƴan asalin garuruwan Ebu da Dzakan da Kpada da Kuchalu da kuma Sampi ne, duk a ƙaramar hukumar ta Patigi.

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

A lokacin da ya yi magana da manema labaru, sarkin Patigi, ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa kimanin mutum 150 ne suka rasa rayukansu, inda aka samu nasarar ceto mutum 53.

Ana yawan samun haɗurran jiragen ruwa a Najeriya, lamarin da kan haifar da asarar rayuka.

Sau da dama akan alaƙanta hakan da ɗaukar mutane a jiragen fiye da ƙa’ida da kuma rashin bin matakan kariya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...