Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya nemi goyon baya da hadin kan bangaren majalisar dokoki ga bangaren zartarwa domin a samu kyakyawar alakar aiki tsakanin su domin ci gaban jihar kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi sabbin shugabanni da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da aka zaba a karkashin jam’iyyar NNNP a karkashin sabon shugaban majalisar Rt. Hon,. Jibril Ismail Falgore wanda ya kai masa ziyara a gidan gwamnati jim kadan bayan an rantsar da majalisar ta goma.
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Gwamnan ya taya sabbin shugabanni da sauran ‘yan majalisar murnar kaddamar da sabuwar majalisar tare da addu’ar Allah Ta’ala ya yi musu jagora wajen sauke nauyin da ke kansu na yin doka da kuma alaka da sauran bangarorin gwamnati cikin kwanciyar hankali da lumana.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
“Muna tabbatar muku da shirye-shiryen gwamnatinmu na yin aiki a matsayin turaku biyu wajen tafiyar da mulki da kuma cigaban jiharmu mai albarka.” inji Gwamnan.
Da take nasa jawabin sabon shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya ce sun ziyarci gwamnan ne domin gabatar masa da sabbin shugabanni da mambobin sabuwar majalisar tare da jaddada aniyar yin aiki da bangaren zartaswa domin cimma burin da ake bukata.
Masarautar zazzau ta bayyana dalilin da yasa ta soke hawan Sallah Babba
A cewar Rt. Hon. Falgore ” Ya mai girma gwamna a wannan gwamnatin taka da bai wuce makonni biyu ba, kayi abubuwan cigaba a kano, wanda hakan ya nuna kana da hangen nesa da Kuma burin cigaban kano, don haka muna bata tabbacin baka hadin kai don dorawa akan aiyukan da kake .” Inji Falgore
Daga cikin tawagar kakakin majalisar akwai mataimakinsa Muhammad Bello Butu-Butu, shugaban masu rinjaye, Lawan Hussani Dala, mataimakin shugaban masu rinjaye, Hon. Garba Shehu Fammar, bulaliyar majalisar Muddasir Ibrahim Zawachiki da sauran ‘yan majalisar.