Sarakunan Kano da Bichi sun jagoranci Jana’izar limamin waje

Date:

Khadija Abdullahi Aliyu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci Sallar Jana’zar Marigayi Limamin Waje Wazirin Kano Murabus Sheikh Nisir Muhammad Nasir.

 

An dai gudanar da Sallar Jana’zar ne da Karfe 9:00am na safiyar ranar Alhamis dinnan ne a Kofar Kudu fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yana daga cikin manyan mutane da suka halarci Jana’zar, da sauran manyan Mutane da Shehunnai da limamai da Yan Kasuwa da sauran al’uma.

 

Bayan idar da Sallar Jana’zar ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauran daruruwan al’umma suka raka gawar Marigayin.

An dai binne marigayi Sheikh Nisir Muhammad Nasir ne a Makabartar Dan Dolo dake Gordon Dutse cikin yankin Karamar Hukumar Gwale dake Birnin Kano.

Mai Martaba Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafarta masa yasa aljanna makoma a gareshi tareda baiwa iyalai da “Yan uwa da sauran al’uma hakurin jure rashin Wazirin Kano Murabus kuma Limamin Waje Sheikh Nisir Muhammad Nasir.

Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano

Kafin rasuwarsa Sheikh Nisir Muhammad Nasir babban Amini ne ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero Wanda ya bayar da gudunmawa a bangaroei daban daban ta hanyar cusa kyawawan dabi’u ga matasa da cusa musu soyayyar Annabi Muhammadu SAW.

Sheikh Nisir Muhammad Nasir ya rasu yabar matansa na aure da Yaya da kuma jikoki masu yawa.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Babban Sakataren yada labarai na Masarautar Kano.
8/6/2023

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...