Daga Umar Sani Kofar Na’isa
An rantsar da sababbin Yan majalisar dokoki ta goma a jihar Kebbi, wanda aka gudanar a chamber majalisar dokoki ta Jihar yau alhamis 8/6/2023.
Bayan rantsar da majalisar ta goma ‘yan majalisun sun zabi Hon. Muhammad Usman, daga yankin Zuru a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar ta goma.
Sannan kuma sun zabi Hon. Samaila Muhammad daga yankin Bagudo ta Gabas a matsayin mataimaki.
Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano
Bikin Rantsuwar ya samu halartar manyan baki da wurare daban daban a ciki da wajen jihar.