Tuna baya: Shekaru tara da rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero – Abubakar Balarabe K/Na’isa

Date:

Daga Abubakar Balarabe Kofar Na’isa

 

A irin wannan ranar ne a Shekara ta 2014, Allah ya karbi rayuwar marigayi mai martaba sarkin Kano Alh Ado Dr. Bayero, marigayi sarkin Kano Alh. Ado Bayero dan sarkin Kano Alh Abduullahi Bayero dan sarkin Kano Abbas dan sarkin Kano Abduullahi Maje Karofi dan sarkin Kano Mallam Ibrahim Dabo.

 

Kazalika, marigayi mai martaba sarkin Kano Alh Dr. Ado Bayero CFR shi ne sarkin Kano na goma sha uku (13) a jerin Sarakunan Fulani a Kano, kuma sarkin da yafi kowani sarki dadewa a kan karagar sarautar Kano, Alh Dr. Ado Bayero CFR, LLP, JP, (malfar sarakunan Kano) ya yi shekaru hamsin da daya (51) yana sarautar Kano.

Da dumi-dumi: Majalisar Dattawa ya Amincewa Tinubu ya nada masu Shawara na Musamman 20

Bugu da kari marigayi mai martaba sarkin Kano Alh Ado Bayero CFR mutum ne mai hakuri da son jama’a ga kawaici ga zumunci da son al”ummar shi. Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayero (Takawa) ya yi zamani da Gwamnoni daban-daban a tsawon mulkisa wanda ya shafe shekaru hamsin da daya (50) tun daga mulkin Farar hula har zuwa Soji’ Kai har da yan sanda duk ya yi zamani dasu, kuma ya hadu da kalubale iri daban-daban amma cikin hukucin Allah Ta’ala duk an yi an gama lafiya, ga shi yau sai tunashi akeyi da irin abubuwan alheri da ya assasa.

Kasancewarsa Shekaru Tara kenan da rasuwarsa, Kungiyoyi da dai daikun al’uma sunata shirya addu’oi da ta’aziyyarsu ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da iyalan gidan Dabo da al’umar jihar Kano bisa rashin babban Bango bajimi uban Sarakuna masoyin al’uma da fatan Allah ya jaddada masa rahama ya cigaba da raya zuriyarsa yayi mata albarka.

 

Ko shakka Babu tarihin Kano bazai taba cika ba sai an Sanya sunan marigayi Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayero sakamakon irin gudunmawar da ya bayar wajan cigban al’uma da da bada ahawarwari ga masu Mulki na soja dana siyasa da yan kasuwa da Attajirai domin dai bunkasa jihar Kano haar takai a inda take a yanzu.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to Kano Emirate Council.
6/6/2023

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...