Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake yanke hukunci alƙalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci masu ƙarar da kowannensu ya biya naira miliyan 10 ga ministan shari’a kuma Atoni janar na Nigeria .
Ba za mu amince da ƙaƙabawa majalisa ta 10 shugabanni ba- Zaɓaɓɓun Sanatoci
Masu ƙarar dai na iƙirarin cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a baban birnin tarayyar Abuja ba, dan haka suke ganin bai cancanci zama shugaban ƙasar Nigeria ba.
Mai shari’a Ekwo ya ce masu karar ba su da ‘yancin shigar da ƙarar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne kawai ya kamata a shigar da ƙasar, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.