Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin rushe duk wani gini da ka gina shi ba bisa ka idaba a fadin jihar.
” Zamu rushe duk wasu gine-gine da aka yi a makarantu, makabartu, asibitoci da masallatai da dukkanin Inda basu dace ba, saboda kawata kano da kuma dawo da kimar jihar a idon Kano”. Inji Abba Gida-gida
Gwamnan ya bayyana haka ne a a wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
KAYYASA: Kalli yadda Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya fara rushe gine-gine (hotuna)
” Wannan aiki da zamu yi zai bamu damar dawo da kimar Kano da Kuma dawo da harkokin gwamnati a wurare kamar yadda suke tun a baya”. A cewar
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a a safiyar ranar Asabar din nan gwamnatin jihar kanon ta rushe wani gini da aka yi shi a jikin filin sukuwa dake kano.