Daga Rahma Umar Kwaru
Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta bayyana cewa za ta shiga yajin aikin gama gari daga ranar Laraba mai zuwa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tsadar mai a fadin kasar sakamakon jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na kaddamar da shi inda ya bayyana cewa ” tallafin man fetur ya kare”.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwar kungiyar ta kasa a Abuja.

Ya ce gwamnati, musamman ma kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da ya dawo da tsohon farashin man zuwa ranar Larabar mako mai zuwa in kuma ba haka ba zasu kirawo yajin aiki a duk fadin kasa.
Ajaero ya kara da cewa rashin cika wa’adin da gwamnatin tarayya ta yi zai janyo zanga-zangar da ba a taba yin irin ta ba a fadin kasar nan.