Dogayen layukan mai sun dawo a gidajen sayar da mai a fadin biranen Najeriya tun bayan da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man.
A jiya Litinin ne Tinubun ya sanar da cire tallafin a jawabinsa na farko bayan rantsuwar kama iaki inda ya ce kasafin ba ya cikin kasafin kudin da ya gada daga gwamnatin Buhari.
Wasu rahotanni na cewa a birane irin su Lagos da Abuja ana sayar da man a wasu wuraren a kan kusan naira 600 a kan lita daya kari daga daga 185 a kan lita a yau Litinin.
Sai dai kuma kamfanin mai na kasar NNPC ya sanar cewa akwai wadataccen mai a kasar saboda haka babu dalilin da zai sa mutane su shiga fargabar sayen man.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Koka da yadda Ganduje ya bar masa bashi Mai tarin yawa
Ζ³an kasar da dama na kokawa kan yadda suke shafe tsawon lokaci a kan layi domin sayen man.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya yi Sabbin nada-naden mukamai
Tinubu ya ce za a yi amfani da kudin tallafi wanda ya ce a yanzu wasu attajirai ne kawai suke cin moriyarsa, wajen bunkasa wasu fannonin da jama’a za su fi amfana.
Ba a san ko tun daga jawabin nasa gwamnati ta dakatar da tallafin ba kenan.
Masana harkokin tattalin arziki na nuna cewa tasirin cire tallafin zai haddasa tsadar sufuri da kayayyaki.