Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sabbin shugabannin hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya yi Sabbin nada-naden mukamai
Wadanda aka nada sun haɗa da Alhaji Yusuf Lawan a matsayin shugaba, sai Alh. Laminu Rabi’u a matsayin babban sakatare.
Sauran sun haɗa da Sheik Abbas Abubakar Daneji, Sheik Shehi Sani Mai Hula, Amb Munir Lawan, Sheik Isma’il Mangu, sai Hajiya Aishatu Munir Matawalle da kuma Dr. Sani Ashir, dukkanin su a matsayin mambobi.
Sanarwar da kakakin gwamnan Sanusi Bature ya fitar, tace naɗin ya fara aiki nan take.
Sanarwar ta ce gwamnan ya bukaci sabbin shugabannin su tabbatar sun yi aiki tukuru don samun nasara gudanar da aikin hajjin bana lafiya.