Yan sanda sun kama fasinjan da ya buɗe kofar jirgin sama ana tafiya

Date:

An kama wani mutum wanda ya bude kofar fitar gaggawa ta wani jirgin sama na kamfanin Asiana Airlines a lokacin da yake shirin sauka a Koriya ta Kudu.

 

Dukkanin fasinjojin jirgin, wanda ya sauka lafiya a babban filin jirgin sama na Daegu, yau Juma’a, su 194 sun fita lafiya duk da kasancewar kofar a bude.

Kungiyar yan Jaridu ta ARTV ta karrama Hadimin Ganduje Aminu Dahiru

Rahotanni sun ce aƙalla fasinja shida sun gamu da matsala ta nunfashi inda aka ɗauke su zuwa asibiti.

Jirgin na sauka aka kama mutumin wanda ya bude kofar, ɗan sama da shekara 30

Akwai yara da dama a cikin jirgin da za su je kallon wani wasa da za a yi a ƙarshen mako.

Kungiyar yan Jaridu ta ARTV ta karrama Hadimin Ganduje Aminu Dahiru

Kuma sun firgita sosai inda suka riƙa kuka da karkarwa a lokacin.

Ƴan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related