Kotu ta haɗe shari’ar zaɓen shugaban kasa waje ɗaya

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Kotun da ke sauraren shari’ar zaben shugaban kasa ta Najeriya ta hade kararraki guda uku da ‘yan hamayya suka shigar gabanta a kan sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabarairu wanda hukumar zabe INEC ta bayyana Bola Ahmad Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

A rahoton da kotun mai alkalai biyar ta fitar wanda jagoranta Justice Haruna Tsammani ya karanta yau Talata, ta kotun ta umarci fara sauran korafin su Peter obi da jam’iyyarsa ta Labour a ranar 30 ga watan Mayun nan.

Wadanda suka shigar da kararrakin su ne dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da jam’iyyar, sai Peter Obi tare da jam’iyyarsa ta Labour, sai kuma jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Kotun ta umarci masu karar da su gabatar da korafe-korafensu a cikin mako uku wanda cikin lokacin za ta kirawo masu gabatar da shedar da aka ware guda 50, daga ranar 30 ga watan na Mayu a lokacin da za masu korafin za su fara kiran masu sheda a kuma kammala a ranar 23 ga watan Yuni.

Kotun ta ce za a kammala shari’ar a ranar 5 ga watan Agusta a lokacin da lauyoyn masu karar za su gabatar da jawabansu na karshe a rubuce, daga nan kuma kotun za ta ware ranar da za ta bayyana hukuncinta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...