Ƙungiyar ɗalibai ta yi ƙorafi ga gwamnatin tarayya kan littattafan firamare da ke koyar da batsa

Date:

Kungiyar Daliba Musulmi ta Ƙasa, wato MSSN ta bayyana damuwarta kan sanya abubuwan da suka danganci jima’i a cikin wasu litattafan firamare da sakandare da ake yadawa a Nijeriya.

A wasika mai taken “Saka bayanan Jima’i da Luwadi a Littattafan Firamare da Sakandare na Najeriya: Barazana ga tarbiyya da kuma xin zarafin al’adu/addini,” an aika ta zuwa ga ministan ilimi, Adamu Adamu.

Wasikar, mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar, Qaasim Odedeji, da babban sakataren kungiyar, Abdul Jalil Abdur Razaq, su ka sanyawa hannu kuma mai kwanan wata 15 ga watan Mayu, ta nuna rashin jin dadin ƙungiyar kan yadda ake yaɗa ilimin jima’i a wasu litattafan Lissafi, Turanci, da zamantakewa da ake amfani da su a yawancin makarantun sakandaren Nijeriya.

“Mun yi mamakin abubuwan da ke cikin wasu litattafan Lissafi, Turanci, da Kimiyyar zamantakewa da ake amfani da su a yawancin makarantun sakandaren Najeriya a yau.

An gurɓata waɗannan littattafan na karatu har sun haɗa da abubuwan lalata da batsa don lalata da yara ƙanana.

Da take bayar da misalai, kungiyar ta ce wata tambayar da ake yi wa daliban firamare a wani littafin lissafi ita ce “kwaroron roba 20 a tara da kwaroron roba 5 sannan a ɗebe kwaroron roba 2 daidai ya ke da.”

Sun kara da cewa wasu daga cikin litattafan suna yaɗa zubar da ciki, LGBT, wasa da al’aura, da jima’i cikin kariya.

Sun yi kira ga ma’aikatar ilimi da ta gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa litattafan da ake amfani da su a makarantun Najeriya ba su da abubuwan da ke da illa ga tarbiyyar matasa dalibai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...