Ƴan sanda a Kano sun kama matar da ta caka wa yarinya ƴar shekara takwas wuƙa

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Rundunar yan sandan jihar kano a ta ce sun kama wata mata mai shekara 35 da ake zargi da daba wa wata yarinya wuƙa a karamar hukumar Kumbotso na jihar.

 

Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce matar mai suna Fatima ta ɗauki yarinyar ce zuwa wani gida da ba a kammala ginawa ba, inda ta daba mata wuƙa a wuya da ciki sannan ta gudu ta bar ta a wurin.

Kiyawa ya ce an kuma kama mijin matar, inda ya yi iƙirarin cewa tana da matsalar kwakwalwa tare da cewa bai san wajen da take ba, inda daga bisani kuma aka cafke ta a ranar Alhamis a maɓoyarta a kauyen Dungulmi a karamar hukumar Dutse na jihar Jigawa.

Ya zuwa yanzu dai ƴan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a ranar Lahadi 14 ga watan Afrilun, 2023.

Matar da ake zargi dai ta amsa aikata laifin da ake tuhumarta da shi, inda ta ƙara da cewa ta daba wa yarinyar wuƙa ne don ramuwa, saboda a cewarta mahaifin yarinyar yana bai wa mijinta shawarar cewa ya ƙara aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...