Daga Nazifi Musa Kwankwaso
Dubun wata bazawara mai suna Rahama Sulaiman dake garin Kwankwaso a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano ta cika, bayan da ta sa aka yi garkuwa da ‘yarta domin neman kudin fansa a wajen mahaifin yarinyar.
” A jiya litinin cikin hukuncin Allah aka gano yarinyar, bayan babar ta ta shaidawa mahaifin ta cewa an sace yarinyar lokacin da ta aike ta a cikin garin Kwankwaso, kuma daga bisani aka kirawo uban yarinyar ta wayar salula da ya tura kudin Fansa har Naira Miliyan 3 kafin a Sako yarinyar”. Inji Majiyar Kadaura24
Wani makusancin mahaifin yarinyar da aka yi garkuwa da ita wanda ya nemi kadaura24 ta sakaye sunansa shi ne ya shida mana faruwar lamarin.
Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu Bayan Sun Sha Wani Shayi A Gidan Biki A Kano
Yace wani yaro ne yaji mahaifiyar yarinyar mai tana waya tana cewa a chanzawa ‘yar tata kaya saboda an bayar da cigiyar ta a gidajen radio, sannan ana ta yin addu’o’i a masallatan dake garin .
” Bayan da yaron ya fadi cewa ya ji abun da take fada, sai aka sanar da jami’an ‘yan sanda domin su fadada bincike da gano gaskiyar abun da yaron ya fada, daga ƙarshe dai bayan Rahama Sulaiman ta shiga hannun ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ita tasa aka sace ‘yarta ta”.
Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaɓe ta Kori Koken da aka shigar akan Tinubu
Yace ta ce tasa an sace yarinyar ne saboda tana son shiga wasan Hausa kuma an nemi kudi a wajenta kuma bata da su, hakan tasa ta yanke shawarar yin hakan ko zata sami kuɗin a wajen mahaifin yarinyar, wanda dama tasan yana da wani wani fili da aka taba taya masa shi naira Miliyan 2 da rabin tun kafin ya sake ta.
Yace yanzu haka dai Rahama Sulaiman ta na hannun ‘yan sanda kuma ita yarinyar an karbo ta daga hannun wadanda mahaifiyarta ta hada baki da su suka ajiye ta a wani gida dake unguwar Dorayi a karamar hukumar Gwale.
Don tabbatar da faruwar lamarin kadaura24 ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jihar kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa sai dai bamu Sami ji daga gare shi ba, sakamakon mun kirawo wayarsa bai daga ba, kuma mun tura masa sakon kar- ta-kwana amma har lokacin hada wannan rahoton bamu ji daga gare shi ba.