Daga Isa Ahmad Getso
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke zamanta a Abuja ta dage zaman sauraron karar da jam’iyyar APM ta shigar kan zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa ranar Alhamis.
Mai shari’a Haruna Tsammani ya umurci jam’iyyar da duk wadanda ake kara da su fito da manyan batutuwan da za a tattauna kafin a fara sauraron karar.
Ya kara da cewa za a tantance dukkan aikace-aikacen yayin zaman sauraren karar na gaba.
Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar
Jam’iyyar APM ta hannun lauyoyin ta O.A. Atoyebi (SAN) da S.A.T. Abubakar Esq, sun shaida wa kotun cewa ta amsa tambayoyin da wadanda ake kara (INEC, APC, Tinubu, Shettima da Masari) suka yi kafin sauraron karar a cikin karar da ta shigar.