Daga Halima Musa Sabaru
Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar kano Kuma tsohon dan takarar majalisar tarayya a kananan hukumomin kura madobi da garum mallam Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso yace Shugaban kwamitin karΙar mulki na jam’iyyar NNPP Dr. Baffa Bichi ba shi da ikon da zai kirawo manyan Sakatarori ma’aikatun gwamnatin Kano don amsa tambayoyi .
Jaridar kadaura24 ta rawaito cewa Baffa Bichi ya bayyana cewa nan gaba kadan zasu fara gayyato manyan Sakatarori ma’aikatun gwamnatin Kano don su basu bayanai a kokarin da suke na tattara bayanai, sakamakon gazawa kwamitin mika mulki da gwamnatin Kano ta kafa na basu bayanan da suke bukata.
Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da jaridar kadaura24.
Musa Iliyasu Kwankwaso yace dokar kasa bata baiwa kwamitin karΙar mulki da Baffa Bichi yake yiwa jagoranci damar kiran wasu Mutane da suke ma’aikatan gwamnati ba .
Da dumi-dumi: Yan Sanda a kano sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa da wuka
” Har yanzu Gwamna Ganduje ne gwamnan kano har ranar 29 ga watan mayu Shugaban kasa da gwamnoni sune suke da ikon zartar da hukunci kuma duk abun da suka zartar ya zartu don haka a jira”. Inji Kwankwaso
” Baffa Bichi a rude yake Saboda da a bayan a rana daya sai ya kashe Sama da biliyan 200 , Kuma a kullum sai gwamnoni sun je ofishin sa na jiransa saboda damar da Allah ya bashi, amma yanzu Kwankwaso ya Maida shi baya daga yaronsa ya kuma mayar da shi yaron Abba to abun da yake damunsa kenan”. A cewar Musa Iliyasu
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kara da cewa su a sanin su Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo ne suka ci zaben gwamnan Kano, Kuma suna nan suna bin hakkinsu a kotu sa’annan su na da yaΖinin Allah zai basu nasara a kotun, don haka suke ganin idan ma yan kwankwasiyya sun lalata abubuwa a Kano to zasu gyara idan sun zo.