Asusun Tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, ya yi gargaɗin cewa tashin hankalin da ake fuskanta a duniya, kamar ɓarkewar annobar korona sun daƙile ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da aurar da ƙananan yara a duniya.
Adam A Zango yana neman shawara kan aurar wacce ba musulma ba
A wani sabon rahoto, Asusun UNICEF ta gano cewa a shekaru goma da suka wuce, an samu raguwar aurar da yara ƙanana ‘yan ƙasa da shekaru 18, amma ɓarkewar korona da tashe-tashen hankula, da matsin tattalin arziki da sauyin yanayi sun tilasta wa iyaye aurar da ‘ya’yansu mata tun kafin su girma.
UNICEF ya yi ƙiyasin cewa yara mata miliyan 12, ake aurarwa a duk shekara, inda suka kira matakin da take hakki tare da tauye wa yaran ƙuruciya, kuma lamarin ya fi munana a ƙasashen Afirka, kudu da hamadar Sahara.