Daga Umar Sani Kofar Na’isa
Wasu daliban Najeriya da ke kan hanyar su ta guduwa daga ƙasar Sudan sakamakon tashe tashen hankula sun makale Sahara a ranar Alhamis.
Bayan amince da tsagaita wuta na kwanaki uku da dakarun Sudan da dakarun yan tawayen kasar suka cimma, kasashen na ci gaba da kokarin kwashe ‘yan kasarsu.
Yakin Sudan: An kaiwa daliban Nigeria hari
A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta ce ta saki kudi kimanin Naira Miliyan 150 domin daukar hayar motocin bas guda 40 don jigilar wasu ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa birnin Alkahira na kasar Masar, inda za a kai su yan Najeriyan.
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya halarci Faretin Sojoji Sanye da kakin Soji
Amma wasu daga cikin daliban da aka kwashe sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali akan hanyarsu ta zuwa kasar ta masar.
Wata daliba da abin ya shafa, wadda ta nemi a sakaye sunanta ta , ta ce direbobin sun sha alwashin ba za su karasa da su kasar masar din ba, har sai an kammala biyansu kudaden da aka yi yarjejeniya da su.
“Kafin mu fara wannan tafiya, mun fuskanci abubuwa daban-daban, yanzu haka maganar da nake yi maka mun makale a cikin wata sahara tsawon awanni 5, ba mu san ma Inda muke ba.
“Ba mu da ruwa, Kudinmu ya kare, kuma Direbobin sun ce baza su motsa ko ina da motocin ba,har sai an cika musu kuɗin su dinsu. Mun makale a cikin jeji. Ba mu da komai. Ba mu ma san inda muke ba, kuma muna cikin babban hatsari.”
Sai dai Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), ta ce an shawo kan matsalar kuma an ci gaba da aikin kwashe mutanen.
Kimanin ‘yan Najeriya 5,500 ne da suka hada da dalibai suka makale a birnin Khartoum da wasu garuruwan Sudan sakamakon rikicin da ya barke a kasar.