Nigeria da Kasar Ghana Nada Dadaddiyar Alaka – Sarki Bichi

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

Mai Martaba Sarki Bichi Alh. Nasir Ado Bayero yace Najeriya da Kasar Ghana suna da kyakykyawar alaka ya bangarori da dama wanda suka hada da Kasuwanci da harkoki ilimi.

 

” Akwai alaka mai tsaho tsakanin Nigeria da Ghana ta fuskoki daban-daban musamman a ɓangaren Ilimi da kasuwanci saboda yadda kasashen biyu suke chudanyar juna a tsahon shekaru ba tare da tsayawa ba”. Inji Sarkin

 

Sarki ya bayyana hakan yayi da ya karɓi bakuncin tsohon Minitan harkoki Kasuwanci Kasar na kasar Ghana kuma Dan takarar Shugabanci Kasar Mr Alan John Kwadwo Kyerematen a fadarsa.

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya zama mai baiwa gwamnan kano Abba Gida-gida shawara akan Ilimi

Alh. Nasir Ado Bayero yace shi yana da abokai dama a Kasar ta Ghana wanda sun dade suna hulda tare, ya kuma godewa dan takarar na Shugaban Kasar ta Ghana Mr Alan John Kwadwo Kyerematen bisa ziyara.

A jawabinsa Tsohon Minitan harkoki Kasuwanci kuma Dan takarar Shugaban Kasa a Kasar ta Ghana Mr Alan John Kwadwo Kyerematen yace ya Kawo ziyara fadar Sarki Bichi ne do sada zumunci tare da neman tabaraki Sarkin.

Mr. Alan John Kwadwo Kyerematen ya samu rakiyar Sarki Hausawan Ghana Alh. Muhammad Saidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...