Hukumar kididdiga ta Nigeria ta bayyana adadin masu amfani da wayoyin salula a Kano

Date:

Daga Fatima Kabir Labaran

 

Hukumar ƙididdiga ta Nigeria ta bayyana cewa  layukan wayar salula miliyan 222.6 ake da su a ɗaukacin Najeriya a ƙarshen shekara ta 2022.

 

kadaura24 ta rawaito alƙaluma sun nuna cewa an samu ƙarin layukan wayoyin salula miliyan 27.1 a kan miliyan 195.5 da ake da su a ƙarshen 2021.

 

Hukumar ƙididdiga ce ta fitar da alƙaluman a cikin bayananta kan masu amfani da wayoyin tarho a cikin wani rahoto na watanni ukun ƙarshe shekara ta 2022.

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya zama mai baiwa gwamnan kano Abba Gida-gida shawara akan Ilimi

Rahoton ya kuma ce jimillar masu amfani da intanet sosai ya kai miliyan 154.9 a ƙarshen 2022, idan an kwatanta da miliyan 142 da ake da su a ƙarshen 2021.

Ina tuntuba don samar da Kwararrun mukarrabai kafin a rantsar da ni – Tinubu

Game da ƙididdigar masu amfani da wayoyin salula a tsakanin jihohi, rahoton ya nuna cewa Lagos ce jiha mafi yawan layukan wayar salula da 26.5 a ƙarshen 2022, sai jihar Ogun da ke biye mata da miliyan 13.

Kano ce jihar da ta zo a mataki na uku da layukan wayar salula miliyan 12.4.

Rahoton ya nuna cewa jihar Bayelsa mafi ƙarancin layukan wayar salula da miliyan 1.6 sai jihar Ebonyi mai layukan waya miliyan 1.9, akwai kuma jihar Ekiti mai layuka miliyan biyu.

Haka zalika, ya nuna jihar Lagos ce mafi yawan masu amfani da intanet da miliyan 18.7 sai jihar Ogun mai miliyan 9.2 sai kuma jihar Kano mai miliyan 8.5.

Bayelsa ce jiha mafi ƙarancin masu amfani da intanet da miliyan 1.1, tana ƙasan Ebonyi mai miliyan 1.3 ga kuma Ekiti mai miliyan ɗaya da rabi.

Rahoton ya nuna cewa mafi yawan masu layukan wayar salula a Najeriya da MTN suke aiki a shekara ta 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...