Sallah: Dr. Hussaini ya taya Ganduje da sauran Musulmi Barka da Sallah

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Sakataren zartarwa kuma babban sakatare na hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano Dr. Tijjani Hussaini ya taya Gwamna Dr.Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da ‘yan majalisar zartarwa na jiha, masu ba da shawara na musamman, Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero da sauran al’ummar musulmin kasar nan murnar zagayowar bikin Sallah karama.

Hotuna: Yadda Sarkin Kano ya fito domin Hawan Daushen Karamar Sallah

 

Jami’in yada labaran ma’aikatar Maikudi Muhammad Marafa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

 

Wata mata ta kai karar mijinta kotu bisa zargin kin kaita saudiyya don yin Umrah

Sakataren zartarwa ya kuma yi kira ga al’ummar jihar, da ma’aikatan hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano da su yi amfani da abin da suka koya a lokutan azumin watan Ramadan wajen cigaba da harkokin su na yau da kullum.

 

 

Dr. Hussaini ya kuma yi kira ga al’ummar jihar kano da su kara kaimi wajen baiwa gwamnati gudunmawa ta hanyar kai rahoton duk wani bullar cutar ga ma’aikatan lafiya mafi kusa a yayin bukukuwan Sallah da nufin magance su.

 

Daga nan sai sakataren zartarwa ya yabawa hukumar gudanarwa da ma’aikata a dukkan matakai bisa sadaukar da kai da suke yi wajen gudanar da aikin su, sannan ya bukace su da su kara himma wajen ci gaban hukumar tare da addu’ar Allah ya sa a yi bukukuwan Sallah lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...