Ƙasar Ingila za ta dakatar da daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Najeriya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kasar Burtaniya ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da bai kamata a rika daukar ma’aikatan kiwon lafiya da jin dadin jama’a aiki ba.

 

Birtaniya ta yi gyare-gyare tare dq sabunta ‘Ka’idojin daukar ma’aikatan lafiya da jin dadin jama’a daga kasashen duniya.

Rarara ya bayyana dalilan da suka sa yan sandan dake gadin sa su kai harbi

Nigeria ta fada cikin jadawalin sunayen kasashen da Burtaniya zata daina daukar ma’aikatan ta na lafiya ne saboda rahoton da Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar inda tace Najeriya na bukatar tallafin a ɓangaren kula da lafiya.

Goman ƙarshe: Ya kamata matasa ku kashe Datar wayoyin ku, ku daina kallon TV – Dr. Ali Tamasi

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a watan Maris, hukumar ta WHO ta buga jerin sunayen Masu bukatar agaji, wanda ta kunshi kasashe 55 – ciki har da Najeriya – wadanda ke fama da karancin ma’aikatan lafiya.

 

Gwamnatin Burtaniya ta ce ya kamata a baiwa Najeriya da sauran kasashen da ke cikin sunaye fifiko don bunkasa harkokin ma’aikatan lafiya da tallafin da suka shafi tsarin kiwon lafiya tare da samar da kariya da ke hana daukar ma’aikatansu aiki a kasashen duniya.

 

Duk da haka Burtaniya, ta ce kasashen da abun da dakatarwar ta shafa, bawai ana nufin su daina neman aikin ba, xasu iya yi a ɗai-ɗaikun su amma dai su sani ba za a basu fifiko ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...