Tirela ta ƙwace wa direba ta hallaka wata mata a Neja

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Wata mata ta rasa ranta bayan da tirela ta ƙwace sannan ta afka a kanta a mahaɗar Mobil a karamar hukumar Suleja da ke jihar Neja.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar, Kumar Tsukwam ya faɗa wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne lokacin da tirelar ta fito daga garin Diko zuwa Zuba, inda ta murkushe matar.

Ciyar da Kano Gaba ne ya Kawo Abba Kabir Yusuf, ba Ɗaukar Fansa ba – Alhaji Bashir Abubakar

Ya ce mutane ukun ciki har da karamar yarinya sun samu munanan raunuka, kuma an garzaya da su zuwa babbar asibitin Suleja domin yi musu magani.

Matsayin azumi ga masu aikin ƙarfi a Ramadan

Kwamandan ya ce haɗarin ya afku ne tsakanin tireloli guda biyu sakamakon gudu fiye da kima da direban motar yake yi.

Ya kuma shawarci hukumomi da su gina gadar sama a mahaɗar ta Mobil da ya dangana da tsaunin Zuma da kuma Zuba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...