Ciyar da Kano Gaba ne ya Kawo Abba Kabir Yusuf, ba Ɗaukar Fansa ba – Alhaji Bashir Abubakar

Date:

Daga Muhammad Bashir

 

Jaridar kadaura24 ta samu ganawa da Alhaji Bashir Abubakar guda cikin jiga-jigan tafiyar zaɓaɓɓen gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda akafi Sani da Abba Gida-gida, wanda Kuma shi ne shugaban kungiyar AKY 2023.

 

Ga Kuma yadda tattaunawar mu ta kasance da shi.

 

Tam: Ko za mu iya jin sunan ka, Yallaɓai?

 

Ams: Suna na Alhaji Bashir Abubakar Chairman AKY forum na Abba Kabir Yusuf 2023.

 

Tam: Yaya kake tsakanin ka da zaɓaɓɓen Gwamnan Kano na yanzu, Abba Kabir Yusuf?

 

Ams: Ƙani ne ga Abba Kabir Yusuf kuma Amini sa’anann ya amince dani ɗari bisa ɗari. Ina ba shi shawara a dukkan lokacin da waɗansu abubuwa suka taso daga kan harkar ƴan uwa zuwa kan mu’amala kuma bai taɓa bari na a baya ba. Duk sa’ar da na kawo masa shawara saboda yasan bazan ba shi shawarar abinda zai kawo mia shi matsala ba, yana karɓa hannu biyu-biyu.

 

Jarumar Nollywood, Mercy Aigbe, ta Musulunta

Tam: Game da zaɓen gwamna da akayi a Kano, me za ka iya cewa?

 

Ams: Da farko muna yiwa Allah godiya daya ba mu wannan kyakkyawar nasarar kamar yadda muka samu a 2019.

Ga shi Allah ya maimaita gaskiyar sa, ya sake ƙaddamar da Abba Kabir Yusuf a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano. Muna tabbatar wa da al’ummar jihar Kano cewar da yardar Allah kowa zai ji daɗi.

Tun daga 2019 muka kawo Abba, amma an kawo mana mutane marasa daraja wanda suka kawo matsaloli kuma suka sa Kano a cikin wani yanayi mara daɗi.

Alhamdullillah Allah ya amsa addu’ar al’umma kuma za mu fito ƙwan mu da kwarkwatar mu za mu baiwa shi mai girma zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano shawara yanda zai inganta harkkokin al’umma, sannan ya tafiyar da mulkin sa bisa adalci.

Ba zan biya duk wani bashi da Ganduje ya ciyo bayan zabe ba – Shawarar Abba Gida-gida ga bankuna

 

Tam: Waɗanne irin ƙalubale kuka fuskantar, lokacin zaɓe, a matsayin ku na yan’uwan AKY?

 

Ams: Mun sha ƙalubale musamman mu da muke daga ƙaramar hukumar Gwale, mahaifar Gwamna, wanda kuma shugaban jam’iyya ta adawa muna tare da shi. Mun ga abubuwa da yawa cin zarafi da iyayen mu da ƴaƴan mu, abubuwa kala kala ba wanda bamu gani ba.

 

Amma da yake Allah Shine Sarki Mai Adalci, yau ga shi Ya tabbatar da Abba a matsayin Gwamna a jihar Kano.

Kuma al’umma sun fito sun yi zaɓe kuma muna gode masu, Allah ya saka muasu da alkairi.

 

Tam: Shin kuna da ƙudurin ɗaukar fansa ko ramako akan mutanen da suka ƙuntata maku?

 

Ams: Ba bu maganar ɗaukar fansa, sabida mu Allah ya ba mu nasara, burin mu shine ya kawowa Kano cigaba.

 

Ams: Amatsayin mu na ƴan uwansa duk abinda aka mana: na alheri ko akasin haka, za mu bar mutum da Allah. Ga waɗanda suka nufe mu da alheri kuma, za mu nunkawa masu akan abinda suka mana.

Amma zancen mu bibiyi mutane, domin mu yi masa sharri, babu wannan zancen, mu kawai cigaba ne a gaban mu ba sharri ba. Sabida mu yanzu kowa na mu ne, kuma za mu riƙe shi tsakani da Allah kamar yadda Allah ya damƙawa Abba Kabir Yusuf kujera zai yi adalci daga kan mace har namiji daga babba har yaro.

Tam: To me za ka iya faɗawa mutanen Kano, game da halayen Abba Kabir Yusuf?

 

Ams: Halayyar Engineer Abba Kabir Yusuf, mutum ne wanda yake jajirtacce, kuma mai gaskiya da riƙon amana, kuma shi tunda Allah yasa muka taso amatsayin “yaya” yake agurin mu, ba mu taɓa ganin wani yazo masa da tsegumin wani ba. Hasali ma, shi ba ya son wannan.

Shi kullum abinda yake so a kawo masa shawarar abinda zai yi ya taimaka wa ƴan’uwa wanda zai haɗa zumunci, da kanmu amma sam ba ya son abinda zai wargaza zumuncin mu.

Ina mai tabbatar muku da cewa bama a zumunci ba, al’ummar jihar Kano a wannan karon za su yi dace, za su ce ashe ma da tuntuni Abba Kabir shine Gwamnan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...