Masu sanya ido 138 ne za su yi aiki a zaɓen cike-gurbi na gwamna a Adamawa

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Ofishin Jami’an Sanya Ido na shiyyar Arewa-maso-Gabas da INEC ta tantance ya bayyana cewa zai tura jami’ai biyu a kowanne rumfunan zabe 69 domin sanya ido a zaben cike-gurbi na gwamnan jiha da za a yi ranar 18 ga watan Afrilu a jihar Adamawa.

 

Mukhtar Jada, kodinetan kungiyar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Yola a yau Litinin.

Jarumar Nollywood, Mercy Aigbe, ta Musulunta

Ya ce za’a baiwa jami’ansu dabarun sa ido tare da sanya ido kan yadda ake bin dokokin zabe da kuma tabbatar da cewa ba a yi magudin zabe ba tare da yiwa ‘yan takara adalci.

 

Cikakkun sunayen Alkalan da Aka Zaba Don sauraron kararrakin Zaben 2023

Mista Joda ya bayyana cewa kungiyar za ta kuma hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da hukumomin tsaro domin tabbatar da matakin da suka shirya na sake zaben ya gudana cikin nasara.

 

Ya kuma yi kira ga masu zabe a rumfunan zaben da ya shafa da su kasance cikin lumana, cikin tsari da kuma da’a a yayin gudanar da aikin, yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban dan Adam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...