‘Yan bindiga sun sace dalibai mata guda 2 a Zamfara

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

‘Yan bindiga sun sace ɗalibai mata biyu na jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotonni sun ce ‘yan fashin ɗauke da muggan makamai, sun sace ɗalibai mata guda biyu a ɗakunan kwanansu da ke wajen makarantar.

Kannywood: Hamisu Breaker ya Magantu kan batun gaskiyar soyayyarsa da jaruma Rakiyya Moussa

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ambato kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf na tabbatar wa da dangin ɗaliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar na ƙoƙari wajen kuɓutar da ɗaliban.

Shugaban NNPP na kasa, Farfesa Alkali ya yi murabus

Sanarwar ta ce rundunar ‘yan sandan ta samu labarin sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar.

Tun bayan samun labarin sace ɗaliban ne, rundunar ‘yan sandan ta ce ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya faru, to sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ‘yan fashin sun tsere da ɗaliban, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya tura ƙarin jami’an tsaro domin kuɓutar da ɗaliban, tare da kama ‘yan fashin domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Daga ƙarshe kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron haɗin kai domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...