Daga Safiyanu Dantala Jobawa
An ja hankalin sababbin malaman makarantar firamaren da aka dauka, da su kara taimakawa wajen ciyar da sha’anin ilimi gaba a jihar Kano.
Sakataren ilimi na karamar hukumar Garun mallam, Malam Sani Mato ya yi jan hankalin a taron mika takadar shedar kama aiki ga sababbin malamai wanda gwamnatin Kano ta dauka.
Yace ” gwamnatin jihar Kano ta dauke su ne da nufin cike wasu gurabe na makarantun firamare wanda ake fama da karancin malamai a sakamakon ritaya da rasuwar da wasu malamam makarantun firamare suka yi.
“Sabbin Malaman da aka ɗauka aikin daga karamar hukumar Garum Malam sun kai su 40, wadanda zamu turasu makarantun firamare daban-daban don fara aiki turu”. Inji Sakataren Ilimin
Daga nan ya gargade su da zuwa wajen aiki akan lokaci tare da jajircewa wajen shiga ajujuwa don kara inganta ilimin yara a makarantun da aka tura su da karamar hukumar da jihar kano baki daya.
A nasa sakon, shugaban karamar hukumar Garun mallam, Mudansur Aliyu Dakasoye wanda ya samu wakilcin Ahmad Isa Bagio, ya ce “wajibi Sabbin Malaman su yi aiki tukuru don samar da al’umma mai ilimi mai nagarta.

Yace karamar hukumar da gwamnatin jihar kano zasu cigaba da yin duk mai yiyuwa wajen ganin sun Samar da kayan aikin sa malaman zasu yi amfani da su wajen kyautata Ilimi a makarantun firamaren yankin.

Daya daga cikin wadan da suka sami takardar aikin koyarwar Aminullahi Dakasoye a madadin sauran ya ce “a shirye su ke don kara bunkasa ilimi a karamar hukumar Garun mallam. Sannan sun mika godiyarsu ga maigirma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa aminceawarsa na daukar sababbin malamai don kara inganta ilimi a jihar Kano.
Shugabanin sassa daban-daban ne da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin Ilimi a karamar hukumar Garun mallam ne su ka halasci taron mika shedar kama aikin.