Ƙarancin naira: Ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya sun jingine ƙudurin yajin aiki

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta TUC sun dakatar da ƙudurinsu na tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba saboda ƙarancin takardun kuɗi da ake fuskanta a Najeriya.

 

Ƙungiyoyin biyu sun ce za su sa ido tare da bibiya domin tabbatar da ganin babban bankin ƙasar ya ci gaba da samar da takardun kuɗin ga bankunan kasuwanci don sauƙaƙa wahalhalun jama’a.

 

Sun ce za su sa ido ne tsawon mako biyu domin ganin ko al’amura za su sauya game da ƙalubalen samun takardun kuɗi a hannu.

 

Shugaban NLC, Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo ne suka bayyana hakan a taron da suka gudanar yau Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.

 

Bayan samun bayanai daga rassanta da ke jihohi 36 har da babban birnin tarayyar, NLC ta yanke shawarar jingine yajin aikin da ta shirya yi.

 

Ya ce NLC za ta aiwatar da ƙudurinta bayan cikar wa’adin mako biyun da suka ƙara bayarwa matuƙar ƴan Najeriya suka ci gaba da fuskantar ƙarancin takardun naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...