‘Yan sanda sun kama mutum 781 bisa laifukan zaɓe a Najeriya

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 781, kan laifukan da suka shafi zaɓe a lokacin zaɓukan ƙasar na shekarar 2023.

Babban sifeton ‘yan sandan ƙasar Usman Baba Alkali ne ya bayyana haka ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasar 36, tare da wasu manyan jami’an ‘yan sandan.

Saudiyya ta gargaɗi masu ɗaukar hoto a lokacin ziyarar ibada

Yayin da yake cikakken bayani game da kamun, Baba Alkali ya ce an aikata laifukan zaɓe 145 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda rundunar ta kama mutum 203.

Sai kuma a lokacin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jihohi inda rundunar ta ce an aikata laifuka 304, lamarin da ya sa rundunar ta kama mutum 578.

Babban sifeton ‘yan sandan ya ce rundunar ta shirya ganawa babban sifeton da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasar da kuma sauran manyan jami’an ‘yan sandan, don tattauna barazanar da tsaron ƙasar ke fuskanta.

Wanda a cewarsa ‘yan siyasa ke ƙoƙarin tayar da hatsaniya a ƙasar bayan zaɓukan ƙasar da suka gabata.

Ya kuma yi Allah wadai da ‘yan siyasar da suke ƙoƙarin tayar da hargitsi ta hanyar tunzura jama’a domin cimma wasu muradunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...