Saudiyya ta gargaɗi masu ɗaukar hoto a lokacin ziyarar ibada

Date:

 

Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.

 

Sannan kuma su bi dokoki wajen ɗaurar hotunan.

 

Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasa mai tsarkin.

 

Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji haɗawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu, ba tare da izini ba.

 

Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama’a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama’a a wuraren.

 

A baya-bayan nan dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa ƙasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.

 

Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama ‘Riya’, abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutanen ibadar tasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...